Isa ga babban shafi
Afrika

An rantsar da Macky Sall a wani sabon wa'adin shugabancin Senegal

Shugaban kasar Senegal Macky Sall dake karbar rantsuwar kama aiki a Dakar dake babban birnin kasar ya bayyana cewa a wannan sabuwar tafiya zai kawo gyara ga ayukan Firaministan kasar kamar dai yada ya dau alkawali a lokacin yakin zaben kasar.

Macky Sall Shugaban kasar Senegal a bikin rantsar da shi a Dakar
Macky Sall Shugaban kasar Senegal a bikin rantsar da shi a Dakar REUTERS/Christophe Van Der Perre
Talla

Shugaba Macky Sall mai shekaru 57 dake magana a bikin rantsar da shi a Dakar, ganggamin da ya samu halartar Shugabanin kasashen Afrika, ya sake nada Mahammed Boun Abdallah Dionne a mukamin Firaminista da zai aiki a karkashin fadar Shugaban kasar duk da cewa Mista Sall ya bayyana cewa ayukan Firaministan kasar za su raguwa bayan kawo gyara ga kudin tsarin mulkin kasar .

Shugaban kasar ya bayyana cewa da kan sa ne zai bi didingin ayukan dake tafiya a kasar don ganin a biyawa yan kasar bukatun su kamar dai yada ya dau alkawali a yakin zaben kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.