rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rwanda

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rwanda na makokin mutane dubu 800 da aka hallaka a kisan kiyashin kasar

media
Wasu shugabannin Afrika yayin kunna fitilar makokin na kwanaki 100 kan kisan mutane dubu 800 shekaru 25 da suka gabata AFP

Kasar Rwanda ta kaddamar da zaman makokin kwanaki 100 don tunawa da mutanen kasar sama da dubu 800 da aka hallaka a kisan kiyashin da ya gudana shekaru 25 da suka gabata, abinda ya girgiza Duniya baki daya.


Shugaba Paul Kagame ya kunna fitilar tunawa da mamatan wajen wani biki da ya gudana a Kigali, inda ake zaton an birne akalla mutane dubu 250 da suka mutu a rikicin.

Bikin ya samu halartar shugabanin kasashen Chadi da Nijar da shugaban kungiyar kasashen Afirka Moussa Faki Mahamat da Jean Claude Juncker shugaban kungiyar Turai da Firaministan Belguim, Charles Michel.

Bayan kunna fitilar wadda za ta kwashe kwanaki 100 tana ci, shugaba Kagame ya bayyana cewar, babban abin misali da za’a samu daga labarin Rwanda, shi ne fata mai kyau ga aikin su ke.

A cewarsa babu wata al’umma da ta wuce a gyara ta, haka zalika ba’a taba kawar da mutuncin jama’a baki daya.