Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara

Hare-haren 'yan Bindiga ya hallaka mutane 3000 a Zamfara- Yari

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce akalla mutane dubu 3 da dari 5 da 26 ne suka mutu cikin shekaru 5 da fara rikicin jihar da ya shafi kauyuka kimanin 500.

Zamfara State Governor, Abdul'aziz Yari
Zamfara State Governor, Abdul'aziz Yari elendureports
Talla

Gwamnan jihar ta Zamfara Abdulaziz Yari, a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Gusau babban birnin jihar, ya ce yanzu haka akwai majinyata fiye da dubu 8 da 219 wadanda ya ce dukkaninsu na cikin mawuyacin hali.

Taron wanda ya samu halartar mukaddashin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnati Farfesa Abdullahi Shinkafi ya ce akwai kuma fadin gona akalla kadada dubu 13 da yanzu haka ba a iya noma ta saboda ayyukan ‘yan bindiga.

Cikin jawaban Gwamnan na Zamfara ya ce babu shakka hare-haren ‘yan bindigar ya haddasa koma-baya ga tattalin arzikin jihar wanda ya tilasta kulle kasuwanni da shagunan cinikayya, baya ga tilastawa daruruwan jama’a kauracewa muhallansu.

Abdul’aziz Yari ya ce gwamnatinsa ta tattara bayanan sirri kan hare-haren ‘yan bindigar mai dauke da shafuka dubu 7, wanda ya ce akwai alaka tsakanin hare-haren ‘yan bindigar da Kungiyar Boko Haram.

A cewarsa Gwamnati ta gano wasu sansanin ‘yan bindigar har guda 8 a cikin dazukan kuma ta na fatan Gwamnatin Najeriyar ta dauki matakin kakkabe su cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.