Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya sha alwashin dawo da sauran 'yan Matan Chibok

Dai dai lokacin da ake cika shekaru 5 da sace 'yan matan sakandiren garin Chibok a jihar Borno mai fama da rikicin Boko Haram, gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu ba ta fitar da rai kan cewa nan gaba kadan za ta kammala ceto 'yan matan da suka rage hannun Boko Haram ba.

Wasu daga cikin yan matan Chibok a fadar Gwamnatin Najeriya
Wasu daga cikin yan matan Chibok a fadar Gwamnatin Najeriya REUTERS
Talla

Tun a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne, Mayakan kungiyar ta Boko Haram suka farwa makarantar sakandiren 'yan matan garin Chibok tare da sace dalibai fiye da 200.

Yanzu haka dai akwai dalibai fiye da dari da ke hannun mayakan wanda ake ci gaba da tattaunawa wajen ganin an kammala ceto su.

Gwamnatin Muhammadu Buhari, wadda na cikin alkawuranta na neman zaben shekarar 2015 dawo da 'yan matan na Chibok, ta ce har yanzu ta na ci gaba da kokarin ganin an kammala kubutar da 'yan matan.

Gwamnatin Najeriyar karkashin Jagorancin Muhammadu Buhari 'yan watanni bayan hawanta mulki ta yi nasarar kubutar da wasu tarin 'yan matan na Chibok wadanda wasunsu aka yi musayarsu da wasu mayaka na Boko Haram wasu kuma rahotanni ke nuna cewa an biya kudin fansa kafin kubutar da su.

Sanarwar da Malam Garba Shehu mai Magana da yawun Muhamadu Buhari ya fitar a jiya Asabar, ta ruwaito shugaban Najeriyar na cewa basu fidda ran samun damar kammala kubutar da 'yan matan na Chibok ba.

Tun a wancan lokaci dai akwai wasu 'yan mata daga cikin daliban na Chibok da suka zabi ci gaba da zama tare da mayakan na Boko Haram maimakon komawa ga danginsu.

Akwai dai wasu bayanai da ke nuna cewa gwamnatin Najeriyar na tattaunawa da kungiyar ta Boko Haram don ganin an kammala kubutar da 'yan Matan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.