Isa ga babban shafi
Sudan

AU ta bai wa sojojin Sudan wa'adin mika mulki

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi barazanar dakatar da Sudan daga cikinta, matukar sojoji ba su gaggauta mika ragamar mulkin kasar a hannun farar hula ba.

Kungiyar Tarayyar Afrika ta bai wa sojojin Sudan wa'adin kwanaki 15 domin mika mulki ga farar hula ko kuma a dakatar da kasar daga cikin kungiyar
Kungiyar Tarayyar Afrika ta bai wa sojojin Sudan wa'adin kwanaki 15 domin mika mulki ga farar hula ko kuma a dakatar da kasar daga cikin kungiyar ASHRAF SHAZLY / AFP
Talla

Gargadin kungiyar na zuwa ne a daidai lokacin da wadanda suka jagoranci zanga-zangar da ta yi sanadiyyar faduwar gwmanatin Umar al-Bashir suka bukaci a rusa majalisar mulkin sojin don maye gurbinta da ta farar hula a cikin gaggawa.

Kwamitin Tsaro da Zaman lafiya na kungiyar ta Tarayyar Afirka wanda ya gudanar da zama na musamman a ranar Litinin dangane da batun juyn mulkin na Sudan ya bai wa sojojin wa’adin kwanaki 15 don su mika mulkin ga fararar hula.

Kungiyar ta ce babban abin da al’ummar Sudan ke bukata shi ne mulkn dimokuradiyya amma ba na soji ba, saboda haka rashin mutunta wannan gargadi zai sa a dakatar da kasar bayan cikar wannan wa’adi.

Duk da cewa majalisar mulkin sojin ta aiwatar da sauye-sauye da dama bayan kifar da al-Bashir daga karagar mulki, to amma har yanzu jama’ar kasar na ci gaba da tarzoma musamman a birnin Khartum.

Masu zanga-zangar sun ce, ya zama wajibi a rusa majalisar ta mulkin sojin tare da maye gurbinta da gwamnatin rikon kwarya ta farar hula wadda za a bai wa sojojin damar aikewa da wakili a cikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.