rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru Najeriya BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kamaru za ta maido da 'yan Najeriya dubu 4 gida

media
Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Boko Haram Reinnier KAZE / AFP

Hukumomin Kamaru sun bayyana cewar sun shirya tsaf domin mayar da 'yan Najeriya 4,000 da ke gudun hijira a kasar sakamakon rikicin kungiyar Boko Haram.


Gwamnan Lardin Arewa Mai nisa, Midjinyawa Bakari ya bayyana cewar daga ranar 29 ga watan nan za su fara mayar da 'yan gudun hijirar da ke sansanin Minawao, wadanda suka bayyana aniyarsu ta komawa gida don ratsin kansu.

Bakari ya ce, sun tattauna da hukumomin Najeriya kuma sun amince da shirin mayar da 'yan gudun hijirar da suka fito daga Jihar Adamawa.

Rahotanni sun ce, shirin mayar da 'yan gudun hijirar bai shafi wadanda suka fito daga Jihar Barno ba, saboda rashin kwanciyar hankali a yankunansu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, sansanin Minawao ya karbi baki 'yan gudun hijira 57,000 daga Najeriya.