Uganda na son bai wa al-Bashir na Sudan mafaka
Uganda ta ce a shirye take ta bai wa tsohon shugaban kasar Sudan, Omar Hassan al Bashir mafakar siyasa bayan kifar da gwamnatinsa.
Wallafawa ranar:
Karamin Ministan Harkokin Wajen Uganda, Henry Okello Oryem ya ce, muddin aka gabatar da bukatar bai wa al-Bashir mafaka ga kasar, shugabanninta za su duba bukatar da kuma amincewa da ita.
Ministan ya ce, tsohon shugaban ya taka gagarumar ruwa wajen sasanta rikicin Sudan ta Kudu, saboda haka bai ga dalilin da zai sa Uganda ta hana shi mafaka ba.
Rahotanni daga Sudan sun ce, sojojin da ke mulkin kasar a yanzu, sun tasa keyar tsohon shugaban zuwa gidan yarin Kober da ke birnin Khartoum, kamar yadda iyalansa suka bayyana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu