rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Liberia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Macizai sun hana shugaban kasa zama a ofishinsa

media
Shugaban Liberia, George Weah REUTERS/Thierry Gouegnon

Wasu bakaken macizai biyu sun tilasta wa shugaban Liberia, George Weah ficewa daga ofishinsa , in da ya ci gaba da gudanar da  ayyukan gwamnati daga gidansa na kansa.


Sakataren Yada Labaran Gwamnatin Kasar, Toby Smith ya ce, an ga macizan ne a ginin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar, in da shugaba Weah ke da ofishinsa.

Tuni aka umarci daukacin ma’aika da su kaurace wa ginin har zuwa ranar 22 ga watan Afrilu, lokacin da ake saran kammala feshin kashe kwari kamar yadda Mr. Toby ya bayyana.

Tun shekarar 2006 aka mayar da ofishin shugaban kasa a ginin Ma’aikatar Harkokin Wajen sakamakon wata gobara da ta tashi a kusa da babban ginin ofishin shugaban kasa.

Bayanai na cewa, ma’aikata sun yi kokarin kashe macizan amma ba su yi nasara ba sakamakon yadda macizan suka sulale ta wani rami.