Isa ga babban shafi
Mozambique

Guguwar Kenneth na ci gaba da banna a Mozambique

Al’ummar Mozambique na ci gaba da zaman dar-dar sakamakon fargabar sake fuskantar ambaliyar ruwa, dai dai lokacin da guguwar Kenneth ta lalata fiye da gidaje dubu guda baya ga ruwan saman da aka shafe sa’o’i masu yawa ana tafkawa hade da kakkarfar iska.

Wani yanki da guguwar Kenneth ta lalata a Mozambique
Wani yanki da guguwar Kenneth ta lalata a Mozambique RFI/Gaëlle Laleix
Talla

Yayin mamakon ruwa hade da guguwar da suka gudana jiya dai, dubban mutane sun rasa matsugunansu yayinda wani guda ya rasa ransa baya ga daruruwa kuma da suka jikkata.

Kakkarfar guguwar wadda ta shafe kusan wata guda yankin na fuskantar ta’adinta, a jiya juma’a ta sauya salo, yayinda ta ke gudun kilomita 220 a sa’a guda.

Wannan dai ne kusan karo na 3 da guguwar ke juyowa tare da bannata tarin dukiyoyi tare da hallaka jama'a a kasar ta Mozambique.

Baya ga kasar Mozambique, guguwar ta kuma shafi kasar Zimbabwe da Malawi kasashen da ta yiwa banna mafi muni a tarihin ibtila'in da suka taba fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.