Isa ga babban shafi
Benin-Siyasa

Galibin al'ummar Benin sun kauracewa zaben kasar

Adadin mutanen da suka fito domin kada kuri’unsu a zaben ‘yan majalisar dokokin da aka gudanar jiya lahadi a jamhuriyar Benin bai taka kara ya karya ba, wannan kuwa sakamako ne kan yadda aka hana wa jam’iyyun adawa damar tsayar da ‘yan takara a zaben.

Jami'an zabe kenan da ke zaman dakon masu kada kuri'a a zaben na jiya
Jami'an zabe kenan da ke zaman dakon masu kada kuri'a a zaben na jiya RFI/Carine Frenk
Talla

Ministan cikin gidan kasar Sacca Lafiya, ya ce duk da tashe-tashen hankulan da aka samu a birane 7 na kasar, to amma zaben ya gudana.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa an samu rikici garuruwan Paraku, Tchaourou, Glazoue da kuma Save, inda masu zanga-zanga suka lalala kayayyakin zabe, to sai dai a biranen Cotonou da kuma Porto-Novo ba a samu wasu tashe-tashen hankula ba, kamar yadda wani mai suna Souradji Gonda ya shaida mana.

Akalla mutane miliyan 5 ne ke da zarafin kada kuri'a a zaben 'yan majalisun na jiya mai kujeru 83, wanda kuma jam'iyyu 3 suka fafata ciki har da biyu masu biyayya ga jam'iyya Patrice Talon.

Kafin fara kada kuri'a a rumfunan zaben na jiya, gwamnatin Benin ta yi umarnin katse duk layukan intanet don kaucewa fuskantar rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.