Ghana ta zama kasa ta 2 da ta kaddamar da rigakafin cutar Malaria
Kasar Ghana ta kaddamar da shirin yiwa yara rigakafin kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro ko kuma malaria, a karkashin wani gagarumin shirin da aka kaddamar domin yaki da cutar a duniya.
Wallafawa ranar:
Masu aikin bada rigakafin sun fara bada shi ne ga mutanen da suka fi kowa barazanar kamuwa da cutar da suka hada da mata da jarirai a garin Cape Coast dake da nisan kilomita 150 daga birnin Accra.
Wani likita, Justice Arthur ya bayyana fatar sa na ganin maganin rigakafin ya taimaka wajen dakile yadda cutar ke haddasa rasa rayuka a kasar.
An dai zabi Ghana da Kenya da Malawi ne domin gwajin maganin rigakafin a nahiyar Afirka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu