Isa ga babban shafi
Afrika

Ana ci gaba da tafka ruwan sama a Mozambique

Ruwan sama mai karfi na ci gaba da sauka a yankin arewacin Mozambique, bayan afkawar yankin kasar da mahaukaciyar guguwar Kenneth tayi a kwanakin da suka gabata.`

Wani yanki da ambaliya ta afka a Mozambique
Wani yanki da ambaliya ta afka a Mozambique EMIDIO JOZINE / AFP
Talla

Kakkarfan ruwan saman dai a halin da ake ciki, ya tilasta dakatar da aikin kai ceto ga kauyukan da guguwar hadi da ambaliyar ruwan ta afkawa, rana ta uku a jere.

Zuwa yanzu dai adadin mutanen da Guguwar ta Kenneth ta hallaka a kasar ta Mozambique ya kai 41.

A baya,hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta bada umarnin aikewa da magungunan rigakafin cutar ta kwalara akalla dubu 900 kafin cutar ta kai ga girma zuwa annoba, a tsakanin mutane miliyan 3 da iftila’in ambaliyar ya shafa a kasashen na Mozambique da  Zimbabawe da kuma Malawi.

Jami’an lafiya a kasar ta Mozambique sun ce, yanzu haka suna lura da marasa lafiya akalla dubu 2 da 700 da suka nuna alamun kamuwa da cutar ta Kwalara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.