Isa ga babban shafi
Mali

Mahara sun sake hallaka fararen hula da dama a Mali

Wasu Mahara sun hallaka fararen hula 18 a wani farmakin kwanton Bauna da suka kai sau biyu jere da juna, a ranakun Laraba da Alhamis da suka gabata, a yankin Mopti da ke tsakiyar Mali mai fama da rikici.

Wasu dakarun rundunar sojin kasar Mali.
Wasu dakarun rundunar sojin kasar Mali. Reuters
Talla

Lamarin dai ya auku ne a kauyen Tigula da ke yankin na Mopti, inda wata motar sojin Mali ta taka nakiya a lokacin da take ratsa kauyen a ranar Laraba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun hallaka 12 daga cikin adadin mutanen 18 ne a ranar ta Laraba, a lokacin da suka kusanci wurin da wata nakiya ta hallaka wani sojan kasar Mali.

Ganin cewa an shafe tsawo lokaci ba’a ji duriyar mutanen 12 ba, ya sa wasu ‘yan uwansu guda 6 suka bazama nemansu, inda suna kan kokarin hakan ne suma suka rasa rayukansu a hannun ‘yan bindigar da suka hallaka rukunin farko na fararen hular 12.

Hare-haren masu da’awar Jihadi da wasu kungiyoyin ‘yan bindiga, hadi da rikicin kabilanci, sun dada kamari a kudancin Mali, da kuma yankin Mopti da ke tsakiyar kasar, musamman a watannin farkon wannan shekara, inda a cikin watan Maris, wasu mahara da ake zargin mafarauta ne daga kabilar Dogon, suka hallaka Fulani 160 a kauyen Ogossagou.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.