rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Uganda

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dimokaradiyar Uganda ta shiga mawuyacin hali - Bobi Wine

media
Jagoran 'yan adawa, dan Majalisa Robert Kyagulanyi, da aka fi sani da Bobi Wine a Uganda. AFP/Eric Baradat

Daya daga cikin jagororin ‘yan adawa a Uganda Bobi Wine, ya soki matakin da kotun kolin kasar ta dauka, na kara yawan shekarun da aka kayyade ga masu son shiga takarar kujerar shugabancin kasar.


A watan da ya gabata kotun kolin ta Uganda, ta yanke hukuncin amincewa da gyaran kundin tsarin mulkin kasar, inda aka soke dokar haramtawa duk wanda ya kai shekaru 75 neman shugabancin kasar.

Bobi Wine, wanda aka bada belinshi a ranar Alhamis da ta gabata, bayan shafe kwanaki uku a tsare, saboda jagorantar wata zanga-zanga, ya bayyana hukuncin kotun kolin a matsayin babban koma baya ga kasar Uganda a karkashin mulkin Yoweri Museveni mai shekaru 74.

Wine wanda asalin sunanshi Kyagulanyi Ssentamu, tsohon mawaki ne da a yanzu ya koma siyasa, da aniyar neman kujerar shugabancin kasar, don kawo karshen mulkin shugaba Museveni da yake jagorancin Uganda tun daga shekarar 1986.