rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Algeria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yan sandan Algeria sun damke kanin tsohon shugaban kasa

media
Tsohon shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika tare da kaninsa Sa'id Bouteflika a birnin Algiers. 10/4/2009. Reuters/Zohra Bensemra

Yan Sandan Algeria sun kame Sa’id Bouteflika, kani ga tsohon shugaban kasar Abdulaziz Bouteflika da yayi murabus bisa tilas.


Sa’id Boutaflika ya shafe sama da shekaru 10 a matsayin mai baiwa tsohon shugaba Abdel Azizi Bouteflika shawara, wanda ake ganin ya taka rawa sosai wajen tafiyar da mulkin Algeria, a lokacin da yayansa ya kamu da cutar mutuwar barin jiki a 2013.

Yan sandan na Algeria sun kuma damke wasu tsaffin manyan jami’an sojin kasar guda biyu da ke sashin binciken bayanan sirri, da suka hada da Janar Bachir Athmane Tartag da Muhd Mediene.

Jami'an tsaron sun ce an kame tsaffin kusoshin gwamnatin Bouteflikan ne domin amsa wasu tambayoyi da suka danganci yadda suka tafiyar da mulkin kasar.