Isa ga babban shafi
Afrika ta kudu

ANC za ta sake samun rinjaye a Afrika ta Kudu

Alkalumman farko na sakamakon zaben ‘yan majaliar dokokin Afirka ta Kudu, na nuna da cewa jam’iyyar ANC ta shugaba Cyril Ramaphosa, za ta sake samun rinjaye a zauren majalisar dokokin kasar, duk da cewa abu ne mai yiyuwa ta gaza dawo da illahirin kujerun da take da su a tsohuwar majalisar.

Jam'iyyar Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa za ta ci gaba da jagorancin Majalisar Dokokin Kasar
Jam'iyyar Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa za ta ci gaba da jagorancin Majalisar Dokokin Kasar REUTERS/Sumaya Hisham
Talla

Jam’iyyar ANC da ke kan karagar mulki tun 1994, ta ce tana da tabbacin sake samun rinjaye a cikin zauren majalisar dokokin kasar, duk da cewa shugabannin jam’iyyar sun amince abu ne mai yiyuwa jam’iyyar ta rasa wasu daga cikin kujerunta.

Bayan kirga kashi 2 cikin uku na kuri’un da aka kada, ANC na da 57%, sakamakon da ke tabbatar da cewa Cyril Ramaphosa ne zai ci gaba da shugabancin kasar.

Babbar jam’iyyar adawa ta Democratic Alliance ce ke matsayi na biyu da sama da kashi 22%, kuri’un da suka zarta wadanda jam’iyyar ta samu a zaben shekara 2014. Yayinda Freedom Figthers ta Julius Malema da ke jagorantar wani bangare na ‘yayan jam’iyyar ANC da suka balle ke da kusan kashi 9%.

A zaben da aka gudanar shekara ta 2014, jam’iyyar tsohon shugaba Nelson Mandela ta samu sama da kashi 62% na kujerun da ake da su a majalisar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.