rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sudan: Sojoji sun jikkata masu zaman dirshan da dama a Khartoum

media
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Sudan, bayan bude wuta kan masu zaman dirshan da sojoji suka yi a birnin Khartoum. AFP / Sami Mohammed

Mutane da dama sun jikkata a Sudan, sakamakon bude musu wuta da ake zargin wasu sojoji sun yi a yau Laraba, yayinda suke gudanar da zaman dirshan a babban birnin kasar Khartoum.


Wani shaidar gani da ido, Mohammed Dahab ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, lamarin ya auku ne a lokacin da masu zanga-zangar suka yi dandazo a gaf da harabar hedikwatar rundunar sojin kasar da ke tsakiyar birnin Khartoum.

Zaman dar dar a kasar ta Sudan ya sake bayyana ne a dai dai lokacin da ake sa ran soma tattaunawa tsakanin wakilan gwamnatin sojoji mai rikon kwarya, da kuma bangaren farar hula da suka jagoranci, zanga-zangar da ta kawo karshen mulkin tsohon shugaban kasar ta Sudan Omar al-Bashir.

A baya bayan nan dai Sojoji da kuma jagororin masu zanga-zangar neman sauyi a Sudan suka cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin riko wadda za ta share tsawon shekaru uku kafin shirya sabbin zabubuka a kasar.

Janar Yasser Atta, mamba a majalisar koli ta mulkin sojin kasar ne ya sanar da kulla wannan yarjejeniya bayan share tsawon kwanaki ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.