Isa ga babban shafi
Togo

Togo za ta yi zaben 'yan majalisu na farko cikin shekaru 30

Hukumar zaben kasar Togo ta fara tantace sunayen masu kada kuri’u dangane da shirin zaben ‘yan majalisun da za’ayi ranar 30 ga watn Yuni mai zuwa, wanda shi ne irinsa na farko a cikin shekaru 30.

Wasu 'yan Togo da ke adawa da mulkin shugaban kasar Faure Gnassingbé.
Wasu 'yan Togo da ke adawa da mulkin shugaban kasar Faure Gnassingbé. AFP
Talla

Rabon da a yi zaben ‘yan majalisu a Togo tun shekarar 1987.

Shugaban Jam’iyyar adawa ta National Alliance for Change, Jean Pierre Fabre, yace suna ci gaba da janyo hankalin masu kada kuri’a da su je tashoshin zabe domin tantance sunayensu da kuma karbar katin zabe.

Zalika kungiyoyin fararen hula sun bukaci al’ummar kasar da su yi amfani da ranakun 16 da 1 da kuma 18 da aka basu domin sake rajistar.

Ana saran zaben ‘yan majalisu 1,527 daga mazabu 117.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.