rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Chadi Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Boko Haram ta kashe mutane 13 a Chadi

media
Dakarun Chadi dake fada da mayakan Boko Haram REUTERS/Emmanuel Braun

A gabashin Chadi mutane 13 aka sanar da mutuwar su bayan da mayakan Boko haram suka kai wani kazamin hari a kauyen Cellia dake da nisan kilometa 40 da birnin Bol.


Harin da ya wakana da misalin karfe shida na safiyar Alhamis ,mayakan na Boko Haram sun kashe mai gari tareda cinawa gidaje da dama huta.

Daga cikin mutanen da suka rasa rayukan su ,biyu aka yiwa yankar rago,yayinda rundunar sojan kasar biyo bayan harin ta sanar da ta tura da sojin zuwa yankin .

Akalla mutane 27.000 ne suka rasa rayukan su kama daga shekara ta 2009 ,lokacin da kungiyar ta Boko Haram ta samu shiga kasar ta Chadi.