rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia

Libya Turkiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojin Libya sun samu manyan makaman yakar Haftar

media
Wasu sojojin Libya masu biyayya ga gwamnati mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya Photo: Mahmud Turkia/AFP

Rundunar sojin Libya da ke biyayya ga gwamnatin mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da karbar kayakin yaki ciki har da motoci da manyan makamai a wani mataki na ganin ta hanawa Khalifa Haftar kwace iko da Tripoli babban birnin kasar.


Cikin sanarwar da ta fitar, rundunar sojin ta Libya ta ce yanzu ta na da tarin makaman da za ta kare al’ummar birnin na Tripoli daga mamayar Khalifa Haftar wanda ke rike da kaso mai yawa na yankunan kasar.

Ko da ya ke rundunar sojin ba ta sanar da inda ta samu makaman ba, amma rahotanni na nuni da cewa anga tarin motoci masu silke kirar kasar Turkiyya na sintiri a tsakiyar birnin na Tripoli.