rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za a komawa zaman tattaunawa a Sudan

media
Masu zanga-zanga a kasar Sudan ©REUTERS/Umit Bektas

A yau lahadi ake sa ran sake komawa zaman tattaunawa tsakanin masu zanga-zanga da majalisar sojin dake rike da mulkin kasar Sudan a Khartoum dake babban birnin kasar.


Daga cikin kungiyoyin da aka aikewa da goron gayata za iya zana wakilan kungiyoyin adinai da suka taka gaggarumar rawa a baya. Majalisar sojin kasar ce ta sanar da sake komawa tattaunwa da kungiyoyi da ma jam’iyyu a yau don samar da mafita da za ta kaisu ga samar da Gwamnatin rikon kwariya da za a dorawa nauyin shirya zaben kasar kamar dai yadda jama’a suka yi fata.

Kasar ta Sudan ta fada cikin rikici ne tun bayan saukar Shugaban kasar Omar El Beshir.