rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Masar Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masar: Harin bam ya ritsa da masu yawon bude ido

media
Daya daga cikin motocin da harin bam ya shafa a Giza da kasar Masar. 19/5/2019. REUTERS/Sayed Sheasha

Wani harin bam ya ritsa da wata mota da ke dauke da baki ‘yan yawon bude ido a Giza da ke kasar Masar, inda ya jikkata wasu daga cikin su, ciki har da wasu ’yan Afirka ta Kudu.


Rahotanni sun ce an birne bam din a gefen hanya ne, wanda ya tashi lokacin da motar da ke dauke da mutane 17 ke wucewa.

Jami’an tsaro da hukumomin lafiya sun ce mutane 17 ne suka jikkata, yayinda gwamnatin Afirka ta Kudu ta sanar da cewar Yan kasar 3 daga cikin 28 dake tawagar sun samu raunuka.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da mayaka masu da'awar jihadi ke kai harin da ke rutsawa da masu yawon bude ido ba,lamarin da ke barazanar durkusar da samun kudaden shigar da kasar ke yi daga fannin.