Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Yan bindiga sun sake kai hari kan mujami'a a Burkina Faso

Yan bindiga sun kai hari tare da kashe mutane uku, yayinda suke gudanar da ibada a wata mujami’a da ke Toulfe, a yankin arewacin kasar Burkina Faso a jiya lahadi.

Sojin Burkina Faso yayin atasaye a yankin gabashin kasar.
Sojin Burkina Faso yayin atasaye a yankin gabashin kasar. AFP PHOTO/ISSOUF SANOGO
Talla

Rahotanni sun ce maharan dauke da manyan makamai sun afka wa mujami’ar ce, da misalin karfe 9 na safe, a dai dai lokacin da masu ibada suka taru, inda suka kashe mutane uku nan take.

Farmakin ya zo ne mako daya, bayanda wasu maharan suka hallaka wasu kiristoci mabiya darikar katolika guda 4 a kasar ta Burkina Faso, suma kwanaki kalilan, bayanda aka hallaka wani limamin coci tare da mabiyansa guda 5.

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin hare-haren da ake kaiwa a kasar ta Burkina Faso, sai dai gwamnatin kasar ta dora alhakin akan kungiyoyi masu da’awar jihadi da ke yankin Sahel.

A shekarar 2015, Burkina Faso ta soma fuskantar hare-haren ta’addanci a babban birnin kasar Ouagadugou, daga bisani kuma, hare-haren suka bazu zuwa wasu sassan kasar, musamman yankin gabashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.