Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari bai halarci liyafar cin abincin daren da aka shirya masa ba

Najeriya za ta mori ‘’shekaru masu amfani’’ a lokacin wa’adin mulkin Muhammadu Buhari karo na biyu a cewar mataimakin shugaban Farfesa Yemi Osinbajo.

Shugaba Muhammadu Buhari na sa hannu kan wata takarda bayan ya yi rantsuwar kama aiki
Shugaba Muhammadu Buhari na sa hannu kan wata takarda bayan ya yi rantsuwar kama aiki REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Osinbajo ya furta wadannan kalamai ne a lokacin wata liyafar cin abincin dare da aka shirya domin taya shugaban murna wanda ya yi rantsuwar fara wa’adin mulkinsa na shekaru 4 masu zuwa da aka shirya cikin daren laraba.

Farfesa Osinbajo, ya wakilci shugaba Buhari a wannan biki ne, saboda kasancewar shugaban ya yi tafiya zuwa Saudiyya domin halartar taron kasashen musulmi na duniya OIC.

Mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina, ya ce shugaba Buhari yana alfahri da wannan liyafa da aka shirya masa, saboda haka ne ya tura mataimakinsa domin ya wakikce shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.