Isa ga babban shafi
DR-Congo

Gawar Etienne Tshisekedi ta isa birnin Kinshasa

Jirgin da ke dauke da gawar tsohon madugun 'yan adawar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo Etienne Tshisekedi ya isa birnin Kinshasa a wannan alhamis, inda ake shirin yi masa jana'iza irin ta karramawa.

Akwatin gawar Etienne Tshisekedi, lokacin da aka isa da ita birnin Kinshasa daga Belgique, ranar 30 mayun 2019.
Akwatin gawar Etienne Tshisekedi, lokacin da aka isa da ita birnin Kinshasa daga Belgique, ranar 30 mayun 2019. © REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Tshisekedi, ya rasu ne cikin watan fabarairun shekara ta 2017 a birnin Brussels na kasar Belgium, lokacin da ya je kasar domin duba lafiyarsa, kuma tun a wancan lokaci ne ake kokarin dawo da gawarsa gida domin yi ma ta jana’iza sai a wannan lokaci.

An dai samu rabuwar kawuna ne tsakanin iyalan marigayin da kuma tsohuwar gwamnatin Shugaba Joseph Kabila kan yadda za a dawo da gawar da kuma yadda ya kamata a yi ma ta jana’iza.

To sai dai a zaben da aka yi farkon wannan shekara, dan Tshisekedi, wato Felix Tshisekedi ya yi nasarar lashen zaben shugabancin kasar ta Congo, inda ya sa ya gaggauta dawo da gawar mahaifin nasa daga Belgium domin yi ma ta jana’iza a cikin kasar ta Congo.

An baje akwatin gawar daga yau juma'a har zuwa gobe asabar domin bai wa jama'a damar yi ma ta bankwanan karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.