Isa ga babban shafi
Najeriya

Tiriliyan 11 a matsayin tallafin man fetur cikin shekaru 6

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince a biya bashin Naira milyan dubu 129 a matsayin kudin tallafi ga kamfanonin mai na kasar har guda 67, abin da ke nuni da cewa daga watan Yulin bara zuwa yau, gwamnatin kasar ta biya kamfanonin sama da Naira bilyan 545.

Tankar mai a gaban ginin NNPC a Najeriya.
Tankar mai a gaban ginin NNPC a Najeriya. Getty Images/Suzanne Plunkett
Talla

Majalisar ta amince ta biya wadannan kudade ne bisa shawarar da kwamitin kula da harkokin da suka shafi man fetur a karkashin sanatar Kabiru Garba Marafa ya gabatar.

Wannan dai na nufin cewa Najeriya ta kashe sama da naira tiriliyan 11 domin biyan kudin tallafin man fetur a cikin shekaru 6 da suka gabata kamar dai yadda kwamitin harkokin mai na majalisar ya sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.