rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

OIC Sahel Ta'addanci Najeriya Nijar Chadi Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

OIC za ta tallafawa kasashen yankin Sahel wajen yakar ta'addanci

media
Shugabannin kasashe mambobin kungiyar OIC. Reuters

Kungiyar hadin kan kasashen Musulmi, OIC, ta sha alwashin taimakawa kasashen Afrika na yankin Sahel, musamman Chadi, Nijar, Najeriya da kuma Kamaru, wajen karfafa tsaro, da murkushe ta’addancin da suke fama da shi, da sauran matsalolin tsaro.


Alkawarin na kungiyar OIC na kunshe ne cikin sanarwar da ta fitar, bayan kammala taronta kashi na 14 a ranar asabar, 1 ga watan Yuni na 2019, da ya gudana a birnin Makkah da ke Saudiya.

Kungiyar hadin kan kasashen Musulmin ta bukaci manbobinta su kuma tallafawa kasashen G5 Sahel da ke fafutukar karfafa rundunar soji ta hadin gwiwa da suka kafa,don yakar kungiyoyin ta’adda a yankin.

Wasu batutuwan da taron na OIC ya tattauna akai sun hada da rikicin kasar Libya, tsamin dangantakar Saudiya da Iran, sai kuma rikicin yankin gabas ta tsakiya tsakanin Isra’ila da Falasdinu, wanda kungiyar ta yi Tur da zalincin Isra’ila kan yankin na Falasdinawa.