Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu tayi tur da tsawaita mata wa'adin haramcin sayen makamai

Gwamnatin Sudan ta Kudu, ta yi tur da matakin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, na kara wa’adin takunkumin sayen makaman da aka kakabawa kasar.

Wasu daga cikin samfurin tarin makamai na bindigogi masu sarrafa kansu da kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya haramta saidawa gwamnatin Sudan ta Kudu.
Wasu daga cikin samfurin tarin makamai na bindigogi masu sarrafa kansu da kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya haramta saidawa gwamnatin Sudan ta Kudu. AFP Photo/ASHRAF SHAZLY
Talla

A ranar Alhamis da ta gabata, kwamitin tsaron ya kada kuri’ar amincewa dakara wa’adin takunkumin sayen makamai kan gwamnatin Sudan ta Kudu har zuwa31 ga watan Mayu na shekarar 2020.

Sai dai Ministan yada labaran Sudan ta Kudun Micheal Makuei, ya koka bisa cewa matakin zai karawa ‘yan tawayen da ke ci gaba dayakar gwamnati karfi ne kawai, wadanda suka ki sa hannu kan yarjejeniyar sulhun da gwamnati ta cimma da tsohon madugunsu Riek Machar.

Har yanzu dai Sudan ta Kudu na fama da wasu mayakan ‘yan tawaye da ke karkashin Janar Thomas Swaka, na kungiyar 'National Salvation Front' da ke yankin kudancin kasar.

A baya dai kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya kakabawa Sudan ta Kudu takunkumin sayen makamai ne, domin kawo karshen kazamin yakin basasar da yayi sanadin hasarar rayukan dubban 'yan kasar, da kuma raba wasu miliyoyi da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.