Isa ga babban shafi
Somalia

MDD za ta janye dakaru dubu daga Somalia

Majalisar dinkin duniya ta yanke shawarar janye dakarunta dubu daya da ke rundunar AMISOM, mai aikin samar da tsaro a Somalia, duk da cewa hare-haren mayakan na karuwa a sassan kasar, musamman birnin Mogadishu.

Dakarun majalisar dinkin duniya daga kasar Burundi, yayin sintiri a wajen birnin Mogadishu.
Dakarun majalisar dinkin duniya daga kasar Burundi, yayin sintiri a wajen birnin Mogadishu. Reuters/Feisal Omar
Talla

A shekarar 2007 aka kafa rundunar ta majalisar dinkin duniya da ta kunshi dakaru daga kasashen Burundi, Djibouti, Habasha, Kenya da kuma Uganda, kuma tun daga lokacin suke aikin samar da tsaro a kudanci da kuma tsakiyar kasar Somalia.

A makon da ya gabata mayakan Al Shabaab suka hallaka mutane 5 ciki har da tsohon ministan harkokin wajen kasar, a wani harin bam da suka kai a birnin Mogadishu.

A watan Maris da ya gabata kadai, mayakan na Al-Shabaab sun kai munanan hare-hare guda 2 a birnin Mogadishu, inda suka tarwatsa bama-bamai akalla 28.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.