Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

CAF ta umarci Esperance ta maido da kofin da aka ba ta

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF, ta ba da umurnin a sake buga wasan karshe tsakanin Esperance ta Tunisai da Wydad Casablanca ta Morocco, zubi na biyu na gasar cin kofin zakarun nahiyar da aka yi watsi da shi ana tsakar fafatawa a wani wuri da ba shi da alaka da kungiyoyin biyu.

Esperance ta Tunisia da Wydad Casablanca ta Morocco yayin wata fafatawa
Esperance ta Tunisia da Wydad Casablanca ta Morocco yayin wata fafatawa FETHI BELAID / AFP
Talla

Wannan hukunci dai ya jefa wasan kwallon kafa a nahiyar cikin rudani ana saura ‘yan makonni a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka fadada ta inda kungiyoyi 24 zasu taka rawa a cikin ta, gasar da masar za ta karbi bakonci a wannan wata ta Yuni da muke ciki.

Tun da farko kungiyar kwallon kafa ta Esperance ta Tunisia alkalin wasa ya ba nasara a wasan bayan Wydad Casablanca ta Morocco ta yi watsi da wasan sakamakon rashin na’urar da ke taimaka wa alkalin wasa wato VAR, da za ta tantance wata kwallo da Wydad din ta farke alkalin wasa ya soke.

Masu rike da kofin, Esperance ne ke kan gaba da ci 1-0 a wasan na biyu , kuma 2-1 jimilla, yayin da wasan ya tsaya,bayan jinkiri na mintuna 90, alkalin wasa ya baiwa kungiyar da ke wasa a gida, wato Esperance nasara.

Wani babban jami’i a ofishin shugaban hukumar kwallon kafar Afirka, Hedi Hamel ya ce baya ga rashin cika ka’idoji na wasa, akwai matsala ta tsaro yayin wasan na biyu, lamarin da ya hana a karasa wasan, saboda haka za a a sake wasan bayan gasar cin kofin nahiyar Afirka da za fara daga ranar 21 ga watan Yunin nan zuwa 19 ga watan Yuli.

Bugu da kari, hukumar ta CAF ta umurci Esperance ta dawo da kofin da aka bata, amma rahotanni na nuni da cewa zata kalubalanci hukuncin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.