Isa ga babban shafi
Sudan

Jami'an tsaron Sudan sun tarwatsa masu zanga-zangar bijirewa gwamnati

‘Yan Sandan Sudan sun harba tarin borkonon tsohuwa kan dubban mutanen da suka soma kashin farkon zanga-zangar bijirewa gwamnatin sojin kasar, mako guda bayan hallaka mutane 100 da jami’an tsaron suka yi, yayin tarwatsa masu zanga-zanga a Khartoum.

Daya daga cikin yankunan birnin Khartoum da masu zanga-zanga suka tare hanya.
Daya daga cikin yankunan birnin Khartoum da masu zanga-zanga suka tare hanya. Reuters
Talla

A yau Lahadi dai, daruruwan mutane sun yi amfani da manyan itatuwa da tayoyi, wajen tsare hanyoyi a yankin Bahari da ke arewacin birnin Khartoum, inda suka rika hana mutane zuwa wuraren aikinsu, sai dai nan da nan, yan sandan kwantar da tarzoma suka tarwatsa dandazon masu zanga-zangar.

Jagororin masu zanga-zangar sun ba za su daina boren ko bijirewa gwamnati ba, har sai ranar da sojoji suka mikawa farar hula mulkin kasar.

A karshen mako jami’an tsaron Sudan suka kame wasu tsaffin ’yan tawayen kasar 2, da kuma jagoran yan adawa, sa’o’i kalilan bayan da suka gana da Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed a Khartoum, wanda a ranar Juma’a ya isa birnin domin sansanta shugabannin masu zanga-zangar da bangaren sojoji wajen maido da tattaunawar da suka yi watsi da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.