Isa ga babban shafi
Sudan

An shiga wani yajin aikin gama- gari a Sudan

Yan adawa a Sudan sun kira wani yajin aikin gama gari kama daga yau Lahadi,don tilastawa majalisar Sojin kasar mika mulki zuwa farraren hula.Matakin dake zuwa kwanaki biyar bayan sojojin kasar suka bude huta saman masu zanga-zanga a Khartoum.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Khartoum dake kasar Sudan
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Khartoum dake kasar Sudan ASHRAF SHAZLY / AFP
Talla

Wasu rahotanni daga Khartoum na nuni cewa Jami’an tsaro sun kame wasu tsaffin ’yan tawayen kasar, da kuma jagoran yan adawa.

Duk da kokarin mai shiga tsakani, Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed a Khartoum, wanda a Juma’a ya isa birnin domin sansanta shugabannin masu zanga-zangar da bangaren sojoji don sake maido da tattaunawar da suka yi watsi da ita,kungiyoyi na ci gaba da bayyana damuwa ganin halin da kasar ke ciki yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.