Isa ga babban shafi
Uganda

Annobar Ebola ta hallaka mutum na 2 a Uganda

Ma’aikatar lafiyar Uganda, ta ce wata mata mai shekaru 50 da ta kamu da cutar Ebola a kasar, ta zama mara lafiya ta 2 da ta rasa ranta a dalilin annobar da ta ketara cikin kasar daga Jamhuriyar Congo.

Jami'an hukumar lafiya ta duniyab WHO, tare da wasu likitocin kasar Uganda a asibitin  Bwera da ke gaf da iyakar Jamhuriyar Congo.
Jami'an hukumar lafiya ta duniyab WHO, tare da wasu likitocin kasar Uganda a asibitin Bwera da ke gaf da iyakar Jamhuriyar Congo. REUTERS/Samuel Mambo
Talla

Wani karamin yaro mai shekaru 5 annobar ta soma hallakawa a kasar ta Uganda, wanda a shiga kasar tare da iyayensa daga Jamhuriyar Congo.

Karo na farko kenan da cutar ta bayyana a kasar, bayan sake bullar da ta yi a yankin gabashin makwabciyarta Jamhuriyar Congo, cikin watan Agustan shekarar 2018.

Tuni dai hukumar lafiya ta majalisar dinkinduniya duniya ta yi kiran taron gaggawa sakamakon yaduwar annobar ta Ebola zuwa Uganda.

Majalisar dinkin duniya ta ce za ta sake zaman taro a ranar juma’a don bayyana dokar ta bace kan bullar cutar.

Mutane 2000 ne suka harbu da wannan annoba bayan sake bullar ta a Jamhuriyar Congo cikin watan Agustan bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.