rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Tarayyar Turai Zaben Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

EU ta nemi Najeriya ta yi gyara a tsarin demokradiyya da zabe

media
Akwatinan zabe yayin babban zaben Najeriya na 2019 REUTERS/Nyancho NwaNri

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce Najeriya na bukatar jajircewar siyasa wajen inganta harkokin zabe da dimokiradiyar kasar.


Shugabar tawagar masu sa ido na kungiyar EU da suka kalli yadda zaben Najeriya ya gudana, Maria Arena ce ta bayyana haka yayin ganawa da Majalisar gudanarwar Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Arena ta shaidawa shugabannin Jam’iyyar shirin su na gabatar da cikaken rahoto kan yadda zaben wanna shekara ya gudana da kuma shawarwari guda 30 kan yadda za’a inganta zaben.

Jami’ar ta bukaci fara yi wa dokar zabe gyara da wuri da kuma bai wa mata damar shiga siyasar a dama da su, ganin yadda suka zama yan kallo a zaben da ya gabata.