rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Masar Mohamed Morsi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kungiyar 'yan uwa musulmi ta zargi gwamnatin Masar da kashe Morsi

media
Wasu magoya bayan Hambararren shugaban na Masar, Muhammad Morsi, galibi mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brothers REUTERS/ Mohamed Abd El Ghany

Kungiyar 'yan uwa Musulmi a Masar ta zargi gwamnatin Masar da kashe tsohon shugaban kasa Mohammed Morsi a tsanake.


Kungiyar ta ce da gangan gwamnati ta tsare shugaban cikin daki ba tare da barin wani ya kai gare shi ba da hana shi magunguna da kuma bashi abinci mara inganci.

Shi ma shugaban Turkiya Recep Tayip Erdogan ya zargi shugaban kama karya na Masar da kashe tsohon shugabana kasar, inda ya ce tarihi ba zai taba mantawa da wadanda suka daure shi ba, kuma suka yi barazanar kashe shi ba.

Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani ya bayyana kaduwar sa da mutuwar Morsi, inda ya aike da sakon ta’aziya ga iyalan sa.