rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Ebola Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cutar Kyanda ta fi Ebola barna a Congo

media
Kyanda ta kashe mutane sama da dubu 1 da 500, yayinda Ebola ta kashe dubu 1 da 390 a Jamhuriyr Dimokradiyar Congo REUTERS/James Akena

Gwamnatin Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo ta bayyana cutar kyanda a matsayin annoba bayan alkaluman hukuma sun nuna cewar, ta kashe mutane sama da 1,500, adadin da ya zarce 1,390 da cutar Ebola ta kashe.


Rahotanni sun ce, a daidai lokacin da gwamnati ta mayar da hankali wajen dakile yaduwar cutar Ebola, akalla mutane 87,000 suka kamu da cutar kyanda a fadin kasar, adadin da ya saba da 65,000 da aka gani a bara.

Kungiyar Agaji ta ‘Doctors Without Borders’ ta ce, adadin mutane 1,500 da suka mutu a cikin wannan shekara, an same su ne a cikin watanni biyar da suka gabata, wanda shi ne mafi muni tun shekarar 2012, shekarar da cutar ta yi ta’adi mafi muni a Congo.

Kungiyar ta bukaci hadin kai tsakanin kungiyoyin cikin gida da na kasashen duniya domin bada rigakafi ga yara da kuma kula da wadanda suka kamu da cutar.

Ma’aikatar Lafiya ta Congo ta ce, aikin rigakafin zai shafi yara kusan miliyan guda da rabi, yayinda aka yi wa mutane sama da miliyan biyu rigakafin a watan Afrilu.