rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 38 sun mutu a hari kan kauyuka 2 a kasar Mali

media
Wani bangaren na wuraren da kaddamar da hare-haren STRINGER / AFP

Akalla mutane 38 aka tabbatar da mutuwarsu yayinda wasu da dama kuma suka jikkata a wasu tagwayen hare-hare kan kauyukan Mali da ke tsakiyar kasar Mali.


Harin wanda aka kaddamar kan kauyukan Fulani, kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai shi, sai dai za a iya cewa a ban Mali ta fuskanci mafi munin hare-hare ciki har da wadanda ke da alaka da rikicin kabilanci.

Gwamnatin kasar ta Mali cikin sanarwar da ta fitar ta bayyana harin a matsayin na ta’addanci ta ce an tabbatar da mutuwar mutane 38 amma babu hakikanin adadin wadanda suka jikkata.

A cewar sanarwar gwamnatin, harin ya faru ne a garuruwan Gangafani da Yoro na kabilun Dogon da Fulani da ke tsakiyar kasar ta Mali, wanda da ma kabilu ne da yanzu haka ke fuskantar tsamin alaka da junansu.