rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Nijar ta zartas da sabuwar dokar sanya ido kan addinai

media
Sabuwar dokar ta biyo bayan kazamar zanga-zangar mabiya addinin Islama da ta kai ga kone wata majami'a REUTERS/Tagaza Djibo

Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta amince da sabuwar dokar da ke bayyana yadda ake gina wuraren ibada a kasar, duk da cewa wasu ‘yan majalisa sun nuna dari-dari da daftarin dokar. An dai kada kuri’ar amincewa da ita ne kwanaki biyu bayan wata tarzoma da aka yi a garin Maradi tare da kona wata mujami’a.


Wannan dai doka ce mai kunshe da ayoyi 21, kuma abu na farko ta tanadi bai wa kowa damar yin addininsa ba tare da wata tsangwama ba, tare da karfafa zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai mabambanta.

Har ila yau dokar ta yi bayani filla-filla dangane da abin da ake kira wuraren ibada, kuma wannan ne karo na farko da kasar ta samar da doka da ke bayyana hakan karara.

Dokar ta yi bayani a game da yadda ake gina wuraren ibada, tare da bai wa gwamnatin damar kara sa ido game da inda kungiyoyi ko kuma jama’a ke samun kudaden da suke amfani da su domin gina wuraren ibada a cikin kasar.

Karkashin dokar, ba wanda ke da izinin bude wurin ibada ko kuma koyar da addini sai da amincewar gwamnati, sannan kuma wani bangare na dokar ya bai wa kowane addini damar samun wakilci a majalisar kasa mai koli ta harkokin addini.

Kafin wannan doka dai, akwai wani tsari, da ke sa ido kan lamurran da suka shafi addinin musulunci ne kawai a kasar.