rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Nijar Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya da Nijar sun tsaurara matakan yaki da safarar mutane -Rahoto

media
Rahoton ya sanya kasashen na Najeriya da Nijar a rukuni na biyu wadanda ke kokarin kakkabe ayyukan safarar mutane Photo : Sia Kambou / AFP

Wani rahoton gwamnatin Amurka kan matakan da kasashe ke dauka wajen yaki da safarar mutane, ya nuna yadda kasashen Najeriya da Nijar ke jajircewa wajen bunkasa tsaron iyakokinsu don yaki da safarar mutane, ko da dai rahoton ya ce har yanzu kasashen ba su kai mafi karancin mataki da ake bukata ba.


Cikin rahoton na shekara-shekara da Amurka kan fitar game da kokarin da kasashe kan yi don yakar safarar mutane, a bana rahoton ya kasa kasashen zuwa gida 3, a ciki kuma ya yaba da kwazon kasashen Najeriya da Nijar, wadanda Amurkan ke cewa sun samar da matakan tsaro sai dai har yanzu fa basu kai matakin tsaron da ake bukata ba.

Rukuni na farko a cikin kasashen galibi na Afrika su ne wadanda suka kai matakan tsaron da ake bukata wajen hana safarar mutanen, sai kuma rukuni na biyu da kasashen Najeriya ke ciki wadanda suka dauki matakan hana safarar ko da dai akwai sauran rina a kada, sai kuma rukuni na 3 wadanda Amurkan ke yiwa barazanar fuskantar takunkumai saboda gaza daukar matakan hana safara da mutane.

Cikin rahoton, Amurka ta yabawa Najeriya, kan yadda kasar ta kawo karshen amfani da kananan yara a matsayin sojojin yaki a kungiyoyin tsaro da ke samun goyon bayan gwamnati.

A bangaren Nijar, rahoton ya yabawa gwamnatin kasar kan yadda ta horar da jami’ai na musamman da ke aiki akan iyakokin kasar don yaki da safarar mutane da kuma bautar da kananan yara.

Julie Okah-Donli, babbar jami’ar hukumar da ke sanya idanu kan safarar mutane tare da bautar da kananan yara a duniya, ta shaidawa gidauniyar Thompson Reuters cewa, kasashen na Najeriya da Nijar na aiki matuka sai dai akwai bukatar su kara himma la’akari da yadda su ke matsayin hanyoyin da ake amfani da su wajen safarar bil’adama.