Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan Bindiga sun gindaya sharudodin sulhu a Zamfara

Yan Bindigar Jihar Zamfara dake Najeriya da suka dade suna kai munanan hare hare suna kashe jama’a sun gindaya sharudodin tsagaita wuta da kuma ajiye makaman su.

Matasan jihar Zamfara
Matasan jihar Zamfara Dailytimes
Talla

Kwamishinan yan sandan Jihar, Usman Nagoggo ya bayyana haka yayin gudanar da wani taro da yan Sakai dake kare al’ummomin su daga hare haren.

Kwamishinan yace cikin sharidodin da yan bindigar suka gindaya harda dakatar da yadday Sakan ke kashe Fulani idan sun je kasuwannin kauyuka da kuma barin su,su dinga cin kasuwannin kauyuka kamar kowa.

Nagoggo yace sun shirya ganawar da yan Sakai ne domin samo hanyar yadda za’a kawo karshen yadda ake kashe dan bindiga guda kana kuma su su kashe mutane 30 ko sama da haka.

Sakataren kungiyar yan Sakai a Jihar Zamfara Sani Babbar Doka yace a baya anyi irin wannan sulhu, abinda ya sa suka bayar da makaman da suka mallaka domin kare jama’a, amma kuma su yan bindigar suka bijirewa yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.