Cikin wannan shirin zamu Masar muji inda aka yi rashi a makon mai karewa na tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi, zamu tabo hare-hare da ‘yan bindiga ke kaiwa kasashen Mali Burkina Faso da Niger, daga bisali mu shiga Nigeria.
Sauran kashi-kashi
-
Dubi akan matakin gwamnatin mulkin sojin Nijar na katse huldar aiki da dakarun Amurka
Daga cikin muhimman batutuwan da shirin ya waiwaya a wannan makon akwai matakin Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar na kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasar da Amurka.23/03/202419:13 -
Matakin Najeriya na bude iyakokin da ta rufe tsakaninta da Jamhutiyar Nijar
Daga cikin labarun da shirin ya kunsa a wannan makon, akwai matakin da Najeriya ta dauka na bude iyakokin da ta rufe tsakaninta da Jamhutiyar Nijar, tare da janye baki dayan takunkuman da ta kakaba mata.Gwamnatin Birtaniya ta ce a shirye take ta baiwa ‘yan dubban ‘yan Rwanda da ke neman mafaka fam dubu uku kowannensu, to amma fa a bisa sharadin za su amince a mayar da su gida daga kasar ta Birtaniya16/03/202419:19 -
Wasu daga cikin muhimman labarun da suka wakana a makon da ya gabata
Za a ji yadda aka sake zabar sabuwar ranar gudanar da zaben shugabancin kasar Senegal,Al’ummar Sudan ta Kudu sun tsallake rijiya da baya, domin kuwa aniyar wani sabon mugu da ya bayyana ce ta watse bayanda ya yi kokarin shirya juyin mulki a kasar, duk da cewar har yanzu basu gama murmurewa daga kazamin yakin basasar da ya tagayyara su ba, wato dai ana kukan targade karaya kuma na neman kunno kai.09/03/202420:02 -
Wasu daga cikin muhiman labaren mako daga Rfi- Rikicin jihar Kano
Al’ummar Jihar Kano dake Najeriya sun tashi da labarin murabus din da shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi daga mukamin sa, sakamakon abinda ya kira sanyaya masa gwuiwar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi, wajen sukar yadda suke gudanar da aikin su.Wannan murabus din ta haifar da mahawara mai zafi a ciki da wajen jihar Kano, tare da hudubobi a Masallatan Juma’a dangane da muhimmancin hukumar da kuma rawar da take takawa.Nasirudeen Muhammed zai jagoranci shirin.02/03/202420:21 -
Jana'izar ma'aikacin RFI Hausa, Mahammane Salissou Hamissou a garin Tsibirin Gobir
A jiya Juma'a 17 ga watan Fabrairun 2024 ne aka gudanar da jana'izar ma'aikacin RFI Hausa, Mahammane Salissou Hamissou a garin Tsibirin Gobir, Mahammane Salissou Hamissou wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Larabar da ta gabata sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.17/02/202420:10