Isa ga babban shafi
Mauritania

An soma kada kuri'a a Mauritania

A yau asabar mutanen Mauritania ke kada kuria’a dangane da zaben Shugaban kasar, mutumen da ake sa ran zai taimaka tare ci gaba da tabbatar da tsaro da kuma samarwa yan kasar da kayakin more rayuwa.

Takardun zaben kasar Mauritania
Takardun zaben kasar Mauritania RFI/Paulina Zidi
Talla

Zaben na yau ya kasance na farko da aka taba samu a karkashin turbar dImokuradiyya a wanan kasa da ta yi kaurin suna a juyin mulki kama daga shekara ta 1978 zuwa 2008.

Yan takara biyar za su fafata da junan su don maye gurbin Shugaban kasar mai barin gado Mohamed Ould Abdel Aziz .

Ana dai kalon Shugaban kasar mai barin gado Ould Abdel Aziz a matsayin mutumen da ya taka gaggarumar rawa don tabbatar da tsaro a wannan kasa mai yawan jama’a da kusan milyan 4 da dubu dari biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.