rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Habasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kashe wasu jami'an gwamnatin Habasha a wani yunkurin juyin mulki

media
Wasu daga cikin tsofin yan tawayen Habasha CC BY-SA 3.0/Jonathan Alpeyrie/Wikimedia

Firaministan kasar Habasha sanye da kayan soji ya bayyana a kaffar talabijen inda yake bayyana cewa wasu mutane dauke da bindigogi sun yi yukunrin kiffar da mulki da bai yi nasara ba a yankin arewa maso yammacin kasar, tareda raunata babban hafsan sojan kasar.


Ofishin Jakadancin Amurka dake kasar ya gargadi ma’aikanta sa da yan kasar da su yi taka cancan, yayinda aka sanar da yanke intanet a duk fadin kasar.

Rahotanni na nuni cewa babban hafsan sojan kasar da Shugaban yankin da aka kai wannan hari sun mutu .

A karshe Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya bayyana takaicin inda yake mai nuna damuwa da cewa wannan yukunri na juyin mulki zai mayar da hannun agogo baya ga shirin samar da zaman lafiya mai dorewa a wannan kasa.