Mutane da Ebola ta kashe a Congo sun haura dubu 1 da dari 5
Ma’aikatar lafiya a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ta sanar da karuwar mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar annobar cutar Ebolar da kasar ke fuskanta.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar, ta nuna cewa adadin mutanen da cutar ta hallaka ya karu zuwa mutum dubu 1 da 506 daga watanni goma baya zuwa ranar Lahadi yayinda yanzu haka ake da mutane dubu 2 da 239 da ke fama da cutar.
Ko cikin watan Yunin nan dai akalla wasu iyalai 2 sun rasa rayukansu a Uganda bayan ziyartar ‘yan uwansu a kasar ta Demokradiyyar Congo.
Kawo yanzu dai akalla mutane dubu 141 aka yiwa rigakafin cutar ta Ebola baya ga jami’an lafiya galibi a yankin gabashin kasar da nan ne annobar cutar ta fi tsananta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu