rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru Switzerland Paul Biya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An yi zanga-zangar adawa da gwamnatin Kamaru a Switzerland

media
Shugaban Kamaru Paul Biya AFP

Kimanin mutane 40 ‘yan asalin kasar Kamaru sun gudanar da zanga-zangar adawa da shugaba Paul Biya tare da tayar da yamutsi a wani kasaitaccen Otel da ke birnin Geneva na kasar Switzerland, inda shugaban ke hutawa da uwargidansa.


Mutanen ‘yan asalin Kamaru, mazauna Switzerland sun yi rikici da jami’an da ke tsaren lafiyar shugaba Paul Biya a wani palo na kasaitaccen otel din kafin daga bisani jami’an ‘yan sanda su hallara domin kwantar da hankula.

Mai magana da yawun jami’an ‘yan sandan Switzerland, Jean Philippe Brandt ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, sai da suka kwashe mintuna 30 kafin kwantar da hankula.

Brandt ya ce, mutanen sun yi zanga-zangar adawa da gwamnatin Kamaru ne da shugaba Biya ya kwashe gomman shekaru yana jagoranta.

Jaridar Tribune de Geneva ta rawaito cewa, masu zanga-zangar magoya bayan bangaren ‘yan adawar Kamaru ne da ke gudun hijira a Switzerland.

Jaridar ta ce, tun a ranar Lahadin da ta gabata ne shugaba Biya da ya dare kan mulki tun shekarar 1982 ke cikin Otel din.

Kamfnin Dillancin Labaran Faransa ya tuntubi ma’aikatan Otel din don jin karin bayani game da wannan batu, amma ba su ce uffam ba.