rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tunisia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kwantar da shugaban Tunisaya a asibitin cikin mawuyacin hali!

media
shugaban kasar Tunisa Beji Caid Essebsi REUTERS/Zoubeir Souissi

An kwantar da shugaban kasar Tunisiya Béji Caïd Essebsi a asibiti cikin halin rai kakwai mutu ka kwai a yau alhamis, ranar da aka kai wasu hare haren kunar bakin wake 2 da ya hallaka wani dan sanda guda a birnin Tunis, al’amarin dake tabbatar da sake dawowar tashin hankali a kasar.


Dan shekaru 92, M. Essebsi ya gamu da gagarumar matsalar bugun zuciya ne a jiya alhamis inda aka garzaya da shi a asibitin soja dake Tunis, kamar yadda sanarwar fadar shugabancin kasar na tunisiya ta sanar.

A lokacin da yake musanta rade-radin dake cewa shugaban ya mutu, daya daga cikin mashawartan a fadar shugaban, Firas Guefrech ya sanar ta shafinsa na Twitter cewa shugaban na ci gaba da murmurewa.

Haka shima shugaban gwamnati, Youssef Chahed, da ya ziyarci shugaban a asibiti. Ya yi kiran al’ummar kasar da su guje yada labaran karda kanzon kurege dake jefa rudani cikin zukatan al’ummar kasar

Kafin wannan dai ko a makon da ya gabata sai da aka kwantar da shugaba Essebsi a asibiti

A dai bangaren kuma Kafofin yada labaran kasar ta sun bayyana jita-jitar kwantar da shugaban majalisar dokokin kasar, Mohamed Ennaceur, dan shekaru 85 a sibiti

Sakamakon hare haren kunar bakin waken da suka hallaka dan sanda guda, da kuma kwantar da shugaban kasa aasbiti da aka yi , yasa, shugaban majalisar dokokin M. Ennaceur kiran taron gaggawa na shuwagabanin gungun yan majalisun kasar kasar ta Nusiya domin sanar da su halin da kasar ke ciki