rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika Najeriya Chadi Gabon

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Legas ne birni na 4 mafi tsadar rayuwa a Afirka - rahoto

media
Birnin Lagas a Najeriya ©Reuters/Greg Ewing

Wani rahoton masana tattalin arziki da aka saba fitarwa duk shekara ya bayyana Legas a matsayin birni na 4 mafi tsadar rayuwa a nahiyar Afrika.


Cibiyar Mercer mai hedikwata a birnin New York na Amurka, da ke bincike kan yanayin tattalin arzikin biranen duniya ce ta fitar da rahoton.

Cibiyar ta fitar da rahoton matsayin birane a duniya da kuma nahiyoyin da suke ne ta hanyar nazari kan batutuwan da suka kunshi, yanayin hawa da sauka na hada-hadar kudade, hauhauwar farashin kayan masarufi da sauran al’amuran da suka shafi sufuri da kuma lafiya, sai kuma tsadar samun muhallin zama.

Birnin da yafi kowanne tsadar rayuwa a Afirka shi ne Ndjamena na Kasar Chadi kuma na 11 a duniya, yayinda birnin Kinshasa na Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ke matsayi na 2 a Afirka, na 22 kuma a duniya.

Birni na uku mafi tsadar rayuwar a Afirka shi ne Libreville na Gabon, yayinda yake a matsayin na 24 a duniya.

Birnin Legas a Najeriya ke matsayi na 4 wajen tsadar rayuwa a Afirka, na 25 kuma a duniya.

A matakin duniya kuwa, Singapore shi ne birni mafi tsadar rayuwa, biye da shi babban birnin Faransa, Paris, sai kuma Hong Kong, yayinda birnin Zurich na Switzerland ke a matsayin birni na 4 mafi tsadar rayuwa a duniya.