rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Mali Ta'addanci Sahel

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

MDD na nazarin sanya takunkumai kan 'yan kasar Mali

media
Sojojin Majalisar Dinkin Duniya na Minusma a Konna dake yankin Mopti na kasar Mali MINUSMA/Gema Cortes

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara nazari game da bukatar da Faransa ta gabatar, domin sanya takunkumai a kan wasu mutane biyar da ke haddasa tarnaki wajen samar da zaman lafiya a Mali, cikinsu har da wani dan majalisar dokoki daga jam’iyya mai mulkin kasar.


A ranar Alhamis ne Faransa ta gabatar da wannan bukatar a gaban Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya, dauke da jerin sunayen mutanen biyar, da take neman a sanya masu takunkumai da kuma kwace masu kaddarori saboda suna hana samun zaman lafiya a kasar ta Mali.

Daga cikin mutanen biyar akwai Houka Houka Ag Alhousseini wanda jagoran masu da’awar jihadi ne a Tumbuktu, sai kuma Mahri Sidi Amar Ben Daha wanda ya assasa ayyukan jihadi a garin Gao duk a Arewacin kasar.

Sauran sun hada da Mohamed Ould Mataly wanda dan majalisar dokoki ne daga jam’iyyar mai mulki, sai kuma Mohamed Ben Ahmed Mahri dan kasuwa da ya yi kaurin suna wajen fataucin miyagun kwayoyi tsakanin kasashen Mali, Niger, Mauritania da kuma Burkina Faso.

Na biyar shi ne Ahmed Ag Albachar da ke jagorantar wata kungiyar ayyukan jinkai a Kidal. Mambobi a Kwamitin Tsaron na da damar daukar mataki game da wannan bukata ta Faransa kafin ranar talatar makon gobe.