rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru 'Yan Aware Ta'addanci Paul Biya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan bindiga sun sace jagoran 'yan adawa a Kamaru

media
Jagoran 'yan adawar Kamaru na jam'iyyar SDF Ni John Fru Ndi a lokacin da ya ke kira da gudanar da zanga-zanga a kasar bayan zaben Paul Biya Reuters

Yan bindiga sun sace Ni John Fru Ndi, daya daga cikin jagororin yan adawar Kamaru kuma shugaban jam’iyyar SDF da ke yankin kasar na masu amfani da turancin Ingilishi.


An dai sace jagoran yan adawar ne a gidansa da ke Bamenda, inda gungun maharan suka jikkata mai tsaron lafiyarsa.

Jami’iyyar adawar ta SDF ta ce karo na biyu kenan acikin watanni biyu ‘yan bindiga ke sace jagororinta a yankunan yan aware da ke fafatawa da jami’an tsaron kasar Kamaru.

Ni John Fru Ndi mai shekaru 77, shi ne ya zo na biyu a zaben shugabancin Kamaru na shekarar 2011, da shugaba mai ci Paul Biya ya lashe.

A watan Afrilun da ya gabata ma an taba sace Fru Ndi a garin Kumbo, yayin wani zaman makoki, sai dai bayan wasu sa’o’i aka sake shi.

Jam’iyyar SDF na ci gaba da kira ga shugaban Kamaru Paul Biya kan ya sauka daga mulki, domin bada damar kafa gwamnatin wucin gadi, da za ta warware rikicin yankin yan aware masu neman ballewar yankuna masu amfani da Ingilishi daga kasar.

Sai dai mayakan yan awaren sun fusata da matsayin na jam’iyyar adawa ta SDF, la’akari da cewar ta ki goyon bayan aniyarsu ta ballewa daga kasar ta Kamaru, abinda ya sa masu sharhi ke ganin hakan na da nasaba da yadda yan awaren ke kaiwa jagororin jam’iyyar farmaki.