rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Habasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jami'an tsaro sun kame mutane 250 masu hannu a juyin mulkin Habasha

media
Firaministan Habasha Abiy Ahmed bayan yunkurin juyin mulkin kasar da bai yi nasara ba. REUTERS/Kumera Gemechu

Wasu rahotanni daga Habasha na cewa, yanzu haka kimanin mutane 250 jami’an tsaron kasar suka kame tare da daurewa a gidajen yari, wadanda ake zargin ko dai suna da hannu ko kuma masaniya kan yunkurin juyin mulkin kasar da bai yi nasara ba cikin makon jiya.


Cikin bayanan da Kamfanin yada labaran kasar ya fitar bai fayyace nau’in mutanen da aka kama ba, sai dai kungiyar ci gaban yankin Amhara ta bayyana cewa yanzu haka an kame mambobinta akalla 56 wadanda ake zargi da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin ta shugaba Abiy Ahmed.

Yunkurin juyin mulkin dai na Asabar din da ta gabata, wanda ya faru a birnin Bahir Dar, ya kai ga kisan babban hafson sojin kasar, tare da manyan jami’an soji 3, dai dai lokacin rikicin kabilanci ke neman kawo cikas ga tsare-tsaren Firaminista Abiy Ahmed.